Najeriya za ta bincike mutuwar 'yan mata 26 a teku
Gwamnatin tarayyar Najeriya yta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike game da mutuwar wasu ‘yan mata 26 ‘yan asalin Najeriya da suka rasa rayukansu a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai ta tekun Mediterranean.
Wallafawa ranar:
A jiya ne Kasar Italiya ta gudaanar da jana’izar bai daya ta ‘yan matan a kudancin birnin Salerno, in da wasu limami guda biyu daga bangarorin addinin Islama da Kirista suka jagoranci addu’ar binne gawarwakin matan da aka gaza tantance su.
Darektan Hukumar kKla da kaurar jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya Federico Soda ya ce, ga alama an yi kokarin safarar ‘yan matan ne don tirsasa musu shiga aikin karuwanci a Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu