Bakonmu a Yau
Matsayar Amnesty International kan rusa gidajen al’ummar da ke rayuwa gabar tekun Legas.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:37
Kungiyar Amnesty International ta ce tilas hukumomi a Najeriya su dakatar ta rusa gidajen dubban al’ummar da ke rayuwa a wurare ko yankunan da ke gabar teku a jihar Legas. Kungiyar ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ta yi a Legas, ranar Talata, inda ta ce bayan rusa muhallan mazauna yankunan dubu 30,000, akwai shirin rusa wasu gidajen dubu 300,000 a nan gaba. Nura Ado Suleiman ya zanta da Isa Sunusi, jami’in hulda da jama’a na kungiyar ta Amnesty International, wanda yayi karin haske kan halin da ake ciki.