Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar karbo bashi

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na ya karbo rancen kudi dala biliyan biyar da digo biyar daga ketare, don cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar ta 2017.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Za a yi amfani da kudaden ne domin aiwatar da wasu ayyuka, da kuma biyan basusukan cikin gida da wani bangare na kudaden.

Wasu daga cikin manyan ayyukan da za’a yi amfani da kudaden wajen aiwatar da su, sun hada da gina sabon titin sauka da tashin jirage, a filin jiragen sama na Nmadi Azikiwe da ke Abuja, da kuma ginin tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla a jihar Taraba, wadda zata bada karfin megawatt dubu 3.

Zalika, aiwatar da kwangilar shimfida titunan jiragen kasa na zamani a sassan kasar, na daga cikin manyan ayyukan da za’a yi amfani da bashin wajen aiwatarwa.

Sanata Shehu Sani, shi ne shugaban kwamitin sa-ido kan basusukan da gwamnati ke karba, ya bayyana wa Aminu Manu dalilansu na amincewa da matakin.

00:55

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar karbo bashi

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.