Isa ga babban shafi
Afrika

AFRIMA: Satar fasaha kalubale ne ga mawakan Afrika

Fitattun mawakan Afrika sama da 150 ne suka halarci bikin karrama mawakan nahiyar, da ake yi wa taken AFRIMA, a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Fikin da aka warewa mawakan da zasu cashe abikin karrama mawakan nahiyar Afrika da aka fi sani da Afrima, a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.
Fikin da aka warewa mawakan da zasu cashe abikin karrama mawakan nahiyar Afrika da aka fi sani da Afrima, a jihar Legas da ke kudancin Najeriya. RFIHAUSA/Abdoullahi Issa
Talla

Yayinda yake jawabi a lokacin da ya halarci taron, Akon, mawaki dan kasar Senagal, ya ce bikin karrama mawakan na shekarar bana, zai zama madogara ga ilahirin mawakan nahiyar, kasancewar lokaci ya yi da mawakan Afrika za su amfana da aikin da suke yi.

Akon ya ce babban kalubalen da mawakan nahiyar ke fuskanta a halin yanzu shi ne satar fasha, kasancewa ba’a daukar kwararan matakai kan kare hakkin mallaka.

Daga cikin sauran mawakan da ake sa ran za’a karrama a ranar karshe ta wannan taro, akwai Davido na Najeriya, Fally Ipupa na Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, Dj Arafath na Cote D’ivoire, sai kuma Prosper Menko daga kasar Kamaru.

A bangaren gargajiya kuwa akwai King Wasi’u Ayinde daga Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.