Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: 'Yansanda sun tarwatsa zanga-zangar 'yan Shi'a

'Yan sanda a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi domin tarwatsa zanga zangar mabiya mazhabar Shi'a masu biyayya ga Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wadda ta juye zuwa tashin hankali.

Mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya sun dade suna neman gwamnati ta saki El-Zakzaki.
Mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya sun dade suna neman gwamnati ta saki El-Zakzaki. REUTERS/Stringer
Talla

Wakilinmu ya rawaito cewa tattakin da mabiyan ke yi, zuwa dandalin Unity Fountain domin neman a saki shugabansu daga hannun hukumomin tsaron kasar, ya juye zanga zanga ce, a lokacin 'yan sanda suka yi yunkurin dakatar da su, inda suka nuna turjiya.

Hakan ya sa 'yan sanda suka yi amfani da hayakin mai sa hawaye domin tarwatsa zanga zangar.

Gwamnatin Najeriya na tsare da shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, tun bayan arrangamar da sojoji suka yi da mabiyansa a shekarar 2016, duk da umurnin da wata kotu a Abuja ta bayar na cewa a saki shugaban na IMN da matarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.