Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Kotu ta yi fatali da bukatar tsohuwar ministar mai

Wani alkali a Lagos yayi fatali da bukatar tsohuwar ministan mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke na neman gwamnatin Najeriya ta dawo da ita gida domin fuskantar shari’a kan zargin kwashe dukiyar al’ummar kasar da kuma cin hanc da rashawa da ake yi mata da wasu na kusa da ita.

Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun mai ta Najeriya, a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun mai ta Najeriya, a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan. AFP / Wole Emmanuel
Talla

Alkalin kotun Rilwan Aikawa, ya ce bukatar tsohuwar ministan na kokarin kaucewa shari’a ne a London, saboda haka yayi fatali da ita.

Tun a watan Oktoban shekara ta 2015, jami’an tsaro a birnin London suka kame Diezani, bayan kaddamar da bincike kan yashe biliyoyin daloli na kudin Najeriya, sai dai daga bisani an bada belinta bisa tsauraran matakai na hanata fita daga kasar Birtaniya.

A halin da ake cikin Diezani Alison Madueke ke fuskantar bincike kan almundahana da kudaden al’umma a kasashen Italiya, Birtaniya, Amurka da kuma Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.