Kotun ECOWAS ta bukaci Najeriya ta biya ‘yan Biafra Diyya
Kotun Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta bukaci Gwamnatin Najeriya ta biya diyyar naira biliyan 88 ga mutanen yankin Biafra saboda gazawa wajen kwance bama-baman da aka jibge a Yankin su bayan kammala yakin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Alkalin kotun ya umurci gwamnatin ta bada naira biliyan 50 ga mutanen Yankin da suka fito daga Jihohi 11 da kuma bada Karin naira biliyan 38 da za’ayi amfani da su wajen kwance bama-baman da gina makarantu da kotuna da mujami’u da Masallatai a Jihohin.
Tuni dai Najeriyan ta bayyana gamsuwarta da wannan hukunci tare da alkawarta biyan diyyar.
Alkaluma sun ce akalla mutane miliyan guda ne suka mutu a Yakin Biafra na shekaru 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu