Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

“Ba mu da tabbas kan bullar Karambon Biri a Kano”

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta bukaci mutane da su kawar da fargaba dangane da rahoton bullar cutar Karambon Biri, (Monkey Pox a turance), kasancewar har yanzu ba’a kammala binciken da zai tabbatar da bullar cutar a jihar ba.

Yadda cutar Karambon Biri ta kama wani a nahiyar Afirka.
Yadda cutar Karambon Biri ta kama wani a nahiyar Afirka. © CDC/Brian W.J. Mahy/Handout via REUTERS
Talla

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Kabiru Getso ya ce an dauki jinin wani da ya nuna alamun kamuwa da cutar, an kuma tura zuwa cibiyar binciken cututtuka dake birnin Dakkar na Senegal, nan kuma da makwanni 2 zuwa 3 ake sa ran samun sakamako.

Kwamishinan ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa mai yiwuwa mara lafiyar ya kamu da cutar Farankama ne ba Karambon Biri ba, sai dai tuni aka sanya idanu kan baki dayan mutane 60 da suka yi mu’ammala da mara lafiyar bayanda ya nuna alamun kamuwa da cutar.

Ranar Asabar da ta gabata ne, ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta tabbatar da samun karin mutane 6 da suka kamu da cutar ta Karanbon biri.

Mai Magana da yawun ma’aikatar Mrs Boade Akinola ta ce Karin mutane biyu da suka kamu da cutar sun fito ne daga jiihar Bayelsa, 2 daga Akwa Ibom, yayinda sauran 2 suka fito daga jihar Enugu da kuma garin Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.