Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya zargi 'yan Jaridu da son kai

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zargi ‘yan jaridu dake fifita bukatunsu maimakon al’ummar kasa, bayan sun soke shi kan yadda baya son fayyace manufofinsa ga Faransawa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

A lokacin da yake amsa tambayoyi a ziyarar da ya kai wata makaranta a Gabashin Faransa, macron yace shi bai damu da ‘yan jaridu ba, damuwarsa na tattare ne da Faransawa,

Shugaba Macron na fuskantar matukar koma baya wajen farin jini da kuma karbuwar sa a idan Faransawa sakamakon matakan da sauye sauye da yake dauka, da bai yi musu dadi ba, daga cikin sauye sauyen kuma akwai batun garambawul din da ya yiwa shashin aikin kwadagon kasar.

Wata Kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar ta nuna cewa, a halin yanzu kashi 30 ne kawai na Faransawa suke goyon bayan shugaba Macron, lamarin da karara ya nuna yadda farin jininsa ke dada dusashewa tsakanin al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.