Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta mallakawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 21

Wata Kotu a birnin Legas dake Najeriya, ta mallakawa gwamnatin kasar Dala miliyan 21 daga cikin kudaden da ake zargin tsohuwar ministar mai Dieziani Allison Madukwe da mallake.

Tsohuwar ministar man Najeriya, Diezani Allison-Madueke.
Tsohuwar ministar man Najeriya, Diezani Allison-Madueke. AFP / Wole Emmanuel
Talla

Alkali Abdulaziz Anka, yace kudin ya zama mallakar gwamnatin Najeriya gaba daya kamar yadda Hukumar EFCC ta bukata.

Wannan hukunci ya zo ne kwanaki, bayan da Alkali Anka ya bada umurnin karbe jimillar gidaje 56, da tsohuwar ministar ta mallaka.

Kimanin watanni uku da suka gabata ne dai aka rawaito tsohuwar ministar man na cewa a shirye ta ke ta fuskanci hukuncin zaman gidan yari, bayan ta tona asirin wadanda suka hada kai wajen yashe kudaden al’ummar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.