Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/10 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/10 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/10 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/10 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 18/10 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 18/10 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 18/10 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Ba zamu lamunci yunkurin raba kan kasa ba - Buhari

media Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe yan ta'adda da masu neman raba kan al’ummar kasar.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, shugaban yace ba zasu bari masu fakewa da kabilanci da siyasa su samu damar raba kan yan Najeriya ba.

Bayan sakon godiya ga 'yan Najeriya, shugaban ya bayyana farin cikin sa na komawa gida, inda yace lokacin zaman sa a London yayi ta bibiyan abubuwan dake faruwa a Najeriya, musamman yadda wasu sukayi ta amfani da kafar sadarwa domin neman raba kan kasar.

Buhari yace lokacin da ya yanke hukuncin shigasiyasa a shekarar 2003, tsohon shugaban Yan Tawayen Najeriya, Odumegwu Ojukwu ya ziyarce shi a garin su dake Daura, inda suka kwashe kwanaki biyu suna tattaunawa kan matsalolin Najeriya, kana suka yanke hukuncin cewar babu abinda zai raba kan kasar.

Shugaban yace ba zasu bari wasu bata gari suyi amfani da yan matsalolin da ake da su a kasa wajen neman raba ta ba, kana da zaran an samu matsala su tsallake su bar kasar.

Buhari yace kowanne dan Najeriya na da damar zama a duk inda yake so ba tare da tsangwama ba, kuma idan wasu jama’a na da korafi, suna iy aamfani da Majalisar dokoki ko kuma Majalisar koli domin gabatar da su.

Shugaban ya bukaci jami’an tsaro su murkushe yan ta’adda da masu aikata laifufuka domin a samu zaman lafiya, inda ya sha alwashin magance book haram da masu garkuwa da mutane da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure