Isa ga babban shafi
Najeriya-Lafiya

Najeriya: Kwararru sun kaddamar da bincike kan bakuwar cuta

Cibiyar bincike kan lafiya da kuma kare yaduwar cutuka ta Najeriya, ta kaddamar da bincike kan bakuwar cutar da aka rawaito cewar ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 62 a garin Kogi da ke jihar Kwara.

Wani jami'in lafiya a dakin gwaje-gwaje, da kuma bincike kan cutuka.
Wani jami'in lafiya a dakin gwaje-gwaje, da kuma bincike kan cutuka. gettyimages.co.uk
Talla

Cikin sanarwar da cibiyar ta fitar, ta bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu, domin a cewar ta, binciken da tawagar likitocinta suka yi a karon farko ya nuna cewa, alamun cutar yana kama da na zazzabin Lassa, sai dai kuma bayan zurfafa bincike a dakin gwaje-gwaje, sun gano cewar cutar ba ta zazzabin Lassa ba ce.

Cibiyar Binciken da kuma kare yaduwar cutukan, ta ce tana cigaba da kokarin tantance ainahin cutar da ta bulla a jihar ta Kogi, tare da hadin gwiwar kwararru kan lafiya daga jihar.

A ranar Asabar ne dai Kwamishinan lafiya na jihar ta Kwara, Dr Saka Audu, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, tare da musanta rahotannin cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da bakuwar cutar, ya kai 62.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.