Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasar

Shugaban Najeriya Muhd Buhari ya gana da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da kuma manyan hasoshin tsaron kasar a fadar gwamnatinsa da ke Abuja, bayan komawarsa gida daga birnin London inda ya shafe sama da kwanaki 100 likitoci na kula da lafiyarsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayinda ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin kasar Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayinda ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin kasar Abuja. dailypost.ng
Talla

Babu wani karin bayani kan taron da shugaban ya jagoranta, kasancewar taron na sirri ne.

Jirgin da ke dauke da shugaban kasar ya sauka ne a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A ranar Litinin mai zuwa, 21 ga watan Agustan da muke ciki, ake sa ran shugaban Najeriya Muhd Buhari ya yi wa ‘yan kasar jawabi.

Mai bai wa shugaban shawara na musamman kan kafafen yada labarai Mista Femi Adeshina ne ya tabbatar da hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar.

Daukar lokacin da shugaban yayi kafin dawowarsa, ya haifar da muhawara tsakanin 'yan kasar musamman daga bangaren 'yan adawa.

Ko a farkon makon da ya gabata, sai da wasu suka gudanar da zanga-zanga a garin Abuja inda suke neman shugaban ya koma gida, ko kuma ya gabatar da takardar ajiye aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.