Isa ga babban shafi
Najeriya

"Dole gwamnatin Najeriya ta kare 'yan gudun hijira"

Hukumar jin-kai ta duniya ta bayyana cewa, dole ne gwamnatin Najeriya ta inganta matakan tsaro don kare lafiyar mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Wani sansanin 'yan gudun hijira a garin Maiduguri.
Wani sansanin 'yan gudun hijira a garin Maiduguri. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wannan na zuwa ne bayan mutane 28 sun rasa rayukansu sakamakon wani kazamin hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a sansanin 'yan gudun hijirar a yammacin jiya Talata.

Hukumar ta ce, sansanin ‘yan gudun hijira, wani tudun mun-tsira ne ga mutanen da suka guje wa tashin hankali , amma kuma saboda sakaci, an mayar da sansanin wurin dana tarkon kisa.

Shugaban hukumar reshen Nejariya, Ernest Mutanga ya ce, suna bukatar gwamnatin Najeriya ta kara kaimi wajen kare rayukan fararen hula da ke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijirar.

Mutanga ya kara da cewa, wajibi ne gwamnatin ta sauke wannan nauyi da ya rataya a wuyanta.

Wasu mata uku ne suka kai harin na kunar bakin wake a jiya a Mandari da ke kusa da birnin Maiduguri na jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.