Isa ga babban shafi
Najeriya

MDD ta ce dangantakar ta da Najeriya bai sauya ba

Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu abinda ya sauya dangane da abinda ya shafi dangantakar ta da Najeriya bayan wani samame da sojin kasar suka kai sansanin ta da ke Maiduguri.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Peter Lundberg, shugaban masu aikin jin-kai a Jihar Barno a arewacin Kasar, ya shaidawa manema labarai bayan ganawar da suka yi da Gwamnan Jihar cewar sun warware matsalar da aka fuskanta, saboda haka zasu ci gaba da gudanar da ayyukan su.

Shugaban rundunar zaman lafiya dole, Janar Ibrahim Attahiru ya ce zasu ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya da kuma maganin bata gari.

A Makon da ya gabata, MDD ta ce Jami’an tsaron Najeriya sun abka wani sansanin ma’aikatanta da ke kula da ayyukan jin kai a Maiduguri inda suka gudanar da bincike ba tare da sun sanar da ita ba.

Jami’an tsaron sun shafe sa’o’I uku suna bincike a sansanin a Maiduguri inda wasu bayanai ke cewa sun kaddamar da binciken ne kan labarin da aka yada cewa shugaban Boko Haram ya buya a sansanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.