Isa ga babban shafi
Nigeria

PDP ta amince da wasu kudurori a taronta na kasa

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta kammala taronta na kasa da ta gudanar a yau Asabar a birnin tarayya Abuja.

Sanata Ahmed Makarfi, shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
Sanata Ahmed Makarfi, shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bellanaija
Talla

Taron ya amince da wasu kudurori guda hudu da suka hada da kara wa kwamitin rikon Jam’iyyar da Sanata Ahmed Makarfi ke jagoranta wa’adin watanni hudu don samar da hanyoyin dinke barakar da jam’iyyar ke fama da ita.

Kazalika, taron ya amince da kudirin rusa shugabancin jam’iyyar a wasu jihohin kasar saboda matsalolin da suke fama da su.

Jihohin Bauchi da Borno da Adamawa da Kebbi da Kwara da Ogun da Osun da Lagos na cikin wadanda wannan mataki ya shafa.

A karon farko kenan da PDP wadda ta shafe shekaru 16 akan karagar mulkin Najeriya ta gudanar da taronta na kasa tun bayan kayin da ta sha a zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.