Isa ga babban shafi
Najeriya

Kudaden da muka gano a hannu Diezani somin tabi ne- Magu

Mukaddashin shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu ya ce makudan kudaden da hukumar ta samu daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madukwe bai kai cikin cokali ba daga cikin kudaden talakawan Najeriya da ta yi rub da ciki a kan su.

Mukaddashin Shugaban Hukumar da ke yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya Ibrahim Magu
Mukaddashin Shugaban Hukumar da ke yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya Ibrahim Magu premiumtimesng.com
Talla

Magu ya ce bayan tsananta bincike kan zargin da ake yiwa ministar, EFCC, ta gano tsabar makudan kudaden da suka kai sama da naira biliyan 47 da kuma wasu Dala miliyan 487 da kuma tarin wasu gidaje da kadarorin da ta mallaka.

Shugaban hukumar ya ce suna ci gaba da aiki da wasu hukumomin kasashen duniya domin gano wasu tarin dukiyar da tsohuwar ministar ta mallaka.

Tuni dai kasashen Amurka da Birtaniya suma suka kaddamar da bincike kan ministar saboda zargin halarta kudaden haramun.

Kazalika Magu ya shaida cewa babban kalubalinsa bayan karban wannan aiki shine yadda rashawa ke kokarin yakarsa, sai dai ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da aikin da ya sanya a gaba.

Sau biyu Majalisar dattawan Najeriya ke watsi da bukatar tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.