Isa ga babban shafi
Najeriya

''Buhari bai ta ke doka ba''

Fadar Shugaban Najeriya ta bayyana cewar bukatar wasu ‘yan tsiraru na ganin shugaban kasa ya koma gida ko kuma sauka daga mukamin sa ya saba ka’ida.

Muhammadu Buhari ya yi abinda dokar kasa ta tanada na mika mulki ga mataimakin sa-Fadar Gwamnati
Muhammadu Buhari ya yi abinda dokar kasa ta tanada na mika mulki ga mataimakin sa-Fadar Gwamnati The U.S. | Post-Nigeria
Talla

Mai Magana da yawun fadar Garba Shehu ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi abinda dokar kasa ta tanada na mika mulki ga mataimakin sa saboda haka babu wata doka da ya taka.

Sanarwar da ya rabawa manema labarai ta nuna cewar babu wani gibi da aka samu wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.

Tun kafin cikar shugaban kwanaki 90 da tafiya birnin London ake ta samun musayar kalamai tsakanin wasu daga cikin ‘yan kasar da ke bukatar sani ainihin halin da shugaban ka ciki.

Masanin harkokin shari’a a Najeriya, Ferfessa Shehu Abdullahi Zuru, ya jaddada wa RFI Hausa cewa zaman Shugaban a Birnin London bai saba ka’ida ba, la’akari da cewa ya bar kasar a hannu mataimakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.