Duk da zargi da ake yiwa wasu sojan kasar na take hakkin bil’adama a chan baya, yakan kasance akan bar Hukumar sojan kasar ne su binciki kan su, kuma daga baya su wanke kan su.
Wata sanarwa daga fadar Shugaban kasa tun a jiya Juma’a na cewa Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya kafa Hukumar shari'a da ta kunshi wakilai bakwai karkashin Mai Sharia Biobele A Georgewill na kotun daukaka kara domin bin diddigin zarge-zargen da ake yiwa sojojin kasar na take hakkin bil’adama.