Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 7 a kauyen Adamawa

Wasu da aka ce mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari tare da kashe mutane 7 a kauyen Mildu da ke cikin karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa da ke Najeriya.

Boko Haram ta kai harin ba-za-ta a kauyen Madagali da ke jihar Adamawa
Boko Haram ta kai harin ba-za-ta a kauyen Madagali da ke jihar Adamawa pmnewsnigeria
Talla

Rahotonni sun ce maharan sun kona gidaje da dama a lokacin harin, wanda ya zo wa jama’a da ba-za-ta lura da cewa an jima ba a kai hari a yankin ba.

Wani shaidan gani da ido, mai suna Musa, ya ce mayakan sun dau tsawon sa’a guda suna aikata barna a kauyen, kafin daga bisani mafarauta da soji sun fatatake su.

Shugaban karamar hukumar Madagali, Muhammad Yusuf, ya shaida cewa anyi nasara kashe daya daga cikin Maharan.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan manyan hafsoshin tsaron kasar sun amsa umarni mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, na komawa jihar Borno don kawo karshan yaki da Boko Haram a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.