Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Gwamnatin Najeriya ta maidawa Dasuki martani

Fadar Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da ikirarin tsohon mai bai wa gwamnatin Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, da ke cewa tsohon shugaban ne ya kakkabe mayakan Boko Haram domin gudanar da zaben 2015 a cikin kwanciyar hankali.

Mayakan kungiyar Boko Haram
Mayakan kungiyar Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Mai bai wa gwamnati shawara kan harkokin yadda labarai, Mallam Garba Shehu, ya ce babu gaskiya cikin ikirarin na Dasuki.

Shehu ya ce ko a waccan lokacin, an gudanar da zabukan Najeriya na 2015 ne a mafi akasarin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar Borno, da ma sauran yankunan da ke fama da rikicin kungiyar ta Boko Haram.

Yayinda yake zantawa da sashin Hausa ba RFI, mai bai wa gwamnatin Najeriyar shawara, ya ce idan za’a iya tunawa, har zuwa lokacin dudanar da zaben shugabancin kasar na 2015, akwai sauran yankuna masu yawa da ke karkashin ikon mayakan na Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.