Isa ga babban shafi
Najeriya

A shirye nake na yi zaman gidan yari bayan na tona asiri - Diezani

Tsohuwar ministan albarkatun man Najeriya, Diezani Alion-Madueke, da hukumomin Amurka, Birtaniya, da kuma Najeriyar, ke bincika game da wawashe biliyoyin daloli na kudade, ta yi barazanar tona asirin duk wanda ke da hannu cikin badakalar.

Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun mai ta Najeriya, a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun mai ta Najeriya, a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan. AFP / Wole Emmanuel
Talla

A cewar Alison Madueke, bayan ta kammala bankadar asirin dukkanin wadanda suka hada kai, wajen yin sama da fadi da biliyoyin daloli yayin da take rike da mukamin ministan man Najeriya, a shirye ta ke, a garkame su a gidan yari.

Kalaman na tsohuwar ministan na kunshe ne cikin wani faifan bayaninta da masu gudanar da bincike kan zargin da ake mat a suka nada.

Rahotanni sun ce tuni aka shigar da bayanan cikin bukatar ma’aikatar shara’ar Amurka, na neman kotu ta kwace kudi da kadara da suka kai darajar dala miliyan 144 daga hannun Diezani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.