Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Amfanin noman shukar laimar kwado ga lafiya da tattalin arziki

Wallafawa ranar:

Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako, yayi nazari ne kan noman shukar nan da aka fi sani da Laimar Kwado, wato Mushroom a turance, inda aka gudanar da wani taron bita kan muhimmancin noman wannan albarkar gona a kasar Sin wato China, da kuma yadda za’a bunkasa shi a kasashe masu tasowa. Najeriya na daya daga cikin kasashen da ta samu wakilci a wannan taron bita bisa bunkasa noman laimar kwadon, wadanda suka hada da Sarakuna da kuma Malamai masu nazari kan fannin noman. Shirin na Muhallinka rayuwarka ya samu nasarar tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka samu halartar taron ta manhajar wattssapp. A gefe guda kuma shirin ya karasa kawo muku tattaunawar da yayi da masana da kuma manoma a jamhuriyar Nijar, kan muhimmancin amfani da irin shuka na zamani, wanda ke iya jurewa jinkirin saukar ruwan sama.

Laimar Kwado,Mushroom a turance; irin wadda ta kan tsiro a jeji.
Laimar Kwado,Mushroom a turance; irin wadda ta kan tsiro a jeji. Pixabay
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.