Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisa zata binciki Jonathan kan badakalar Malabu

Majalisar Wakilan Najeriya na shirin gayyatar tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, domin bayyana abinda ya sani dangane da badakalar cinikin rijiyar mai OPL 245 na Dala biliyan 1.3 wadda aka fi sani da Malabu.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ana zargin tsohon shugaban da hannun wajen yarjejeniyar sayar da rijiyar da aka kiyasta cewa na samar da ganga biliyan 9 na danye Mai ga wasu manyan kamfanonin Mai na ENI da Shell a shekarar 2011.

An jima ana tuhumar Kamfanonni biyu da Rashawa, wanda ake bincike a Italiya kan wannan badakalar da ya samu taimakon manyan jami’an gwamnatin kasar.

Kwamiti na musamman da aka kafa don bincike kan al’amari a Majalisar, ya ce akwai bukatar a tasti bayanai daga tsohon shugaban da bincike ya tabbatar da hannusa wajen shirya wannan kwangila.

Kwamitin ya ce zai gayyaci Mista Jonathan ne saboda shi ne shugaban Najeriya a lokacin da aka cim-ma cinikin, wanda kuma ake zargin cewar an yi sama da fadi da dala biliyan daya daga kudin cinikin.

Goodluck Jonathan ya jimma ya na musanta masaniya kan yadda aka cim-ma yarjejeniya da kamfanonin da ke hakar mai a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.