Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Jami'an tsaro sun kame mayakan Boko Haram cikin 'yan gudun hijira

Ma’aikatar bada agajin gaggawa ta jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce an gano wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi badda kama cikin daruruwan ‘yan gudun hijirar da ke komawa Najeriyar daga kasar Kamaru.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu STRINGER / AFP
Talla

Shugaban hukumar ta SEMA, Ahmad Satomi, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, mayakan na Boko Haram 9, da wasu da ke taimaka musu 100 aka damke a cikin ‘yan gudun hijirar akalla 920 da suka koma gida daga garin Marwa na kasar ta Kamaru.

A cewar Satomi, jami’an tsaro sun samu nasarar ce, a lokacin da suke tantance ‘yan gudun hijirar a garin banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Sai dai hukumar bada agajin gaggawar ta Borno ta ce, mai yiwuwa ne da dama daga cikin mutane 100 da aka tsare tare da ‘yan Boko Haram din, an tilasta musu yi wa kungiyar aiki ne, a lokacin da kauyukansu suka kasance a karkashin mamayar mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.