Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

Hukumar binciken sirri ta ta Najeriya DSS, ta sanar da samun nasarar damke wasu ‘yan ta’adda da ke shirya kai jerin hare hare a garuruwan Sakkwato, Kano, Kaduna da kuma Maiduguri, yayin da ake bukukuwan Sallah karama.

Jami'an tsaron hukumar tsaron sirri ta Najeriya DSS.
Jami'an tsaron hukumar tsaron sirri ta Najeriya DSS. Guardian.ng
Talla

Jami’an hukumar sun kame biyu daga cikin wadanda ake zargin, Yusuf Adamu da Abdumuminu Haladu da safiyar wannan Juma’a a garin Sakkwato, kamar yadda jaridar Premium Times da ake wallafata a Najeriya ta rawaito.

Cikin sanarwar da ya fitar a Juma’ar nan, kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo, ya ce tun a makwannin da suka gabata suka samu bayannan sirri da ke cewa, ‘yan ta’addan na shirin kai hare haren bam a sassan Najeriya.

A ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki, hukumar binciken sirrin ta kama wani kwararre wajen hada bama bamai, mai suna Bashir Mohammed a Shekar Madaki da ke karamar hukumar Kumbotso jihar Kano.

Yayin gudanar da bincike kuma jami’an na DSS sun gano manyan bindigogi kirar AK 47 guda takwas, bindigogi masu sarrafa kansu 20, bama-baman gurneti 27, sai kuma alburusai 793.

Zalika jami’an sun kwace tukunyar gas guda, komfutar laptop 3, sai kuma, mota daya da babur din hawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.