Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Matasan Arewacin Najeriya Sun Aikewa Gwamnatin Kasar Budaddiyar Wasika

Wallafawa ranar:

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya, ta rubuta budaddiyar wasika, zuwa ga mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Osinbajo, inda ta bukaci ya baiwa masu fafutukar kafa kasar Biafra, damar yin hakan cikin lumana.Cikin wasikar da kusoshin kungiyar biyar suka sa  hannu, sun yabawa kokarin mukkadashin shugaban, na tattaunawa da kowane bangare don warware takkadamar da ta kaure, sai dai sun ce, ba fa lallai ba ne ya samu nasarar hakan.To idan aka koma ta fuskar doka, ko me kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar dangane da warware irin wannan al’amari ?Nura Ado Suleiman, ya tattauna da Barrister AbdulHameed Muhd, lauya mai zaman kansa da ke Abuja, wanda ya warware zare da Abawa. 

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo rfi
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.