Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

An tabbatar da hukuncin daurin watanni 21 akan Messi

Kotun kolin Spain ta tabbatar da daurin watanni 21 akan dan wasan Barcelona Lionel Messi na Argentina kan badakalar kaucewa biyan haraji a kasar. Wannan na zuwa wata guda bayan gwarzon dan wasan na duniya ya daukaka kara.

Lionel Messi da Mahaifin shi a gaban alkalin kotun Barcelona.
Lionel Messi da Mahaifin shi a gaban alkalin kotun Barcelona. REUTERS/Alberto Estevez/Pool/Files
Talla

An zartar da hukuncin ne akan Messi da mahaifinsa kan laifin boye kudi ta hanyar amfani da wasu kamfanoni a kasashe da dama domin kaucewa biyan haraji a Spain da ya kai kudi euro miliyan 4.16 daga kudaden ya ke samu na tallace tallace tsakanin 2007 zuwa 2009.

Amma a tsarin dokokin Spain za a dakatar da hukuncin, saboda duk wani hukunci na farko da aka zartar kasa da shekaru biyu wanda bai shafi mummunan laifi ba ana dakatar da hukuncin.

Amma duk da haka Messi zai biya kudin tara sama da euro miliyan biyu.

A watan Yuli ne kotun Barcelona ta fara zartar da hukunci akan Messi, kuma kotun ta ce hukunta manyan ‘yan wasa kamar Messi kamar jan kunne ne ga kananan ‘yan wasa game da kaucewa biyan haraji.

Zuwa yanzu dai Messi bai ce komi ba akan ko ya amince da hukuncin, da za a iya dakatarwa kamar yadda ta faru da abokin wasansa Javier Mascherano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.