Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Kano ta dakatar da binciken Sarki Sanusi

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Majalisar Dokokin jihar ta dakatar da binciken da ta ke yi wa masarautar Kano dangane da zargin kashe kudade ba a kan ka’ida ba.

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido Sunusi na II
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido Sunusi na II REUTERS/Joe Penney
Talla

A wasikar da ya aike wa Majalisar Dokokin, gwamna Ganduje ya bukaci a dakatar da binciken ne sakamakon kiraye-kirayen da wasu manyan mutane da suka hada da tsohon shugaban kasar, Ibrahim Babangida da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Aminu Dantata da dai sauransu suka yi.

Gabanin wannan lokaci dai, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauraren korafe-korafen jama’a ta jihar Kano na gudanar da bincike kan Sarki Sunusi bisa zargin sa da barnatar da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 6, zargin da masarautarsa ta musanta.

Hukumar ta fara binciken Sarkin ne bayan wani taro da ya halarta a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, in da ya dora alhakin koma-bayan da yankin arewa ke samu kan rashin jagoranci na gari da kuma son zuciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.