Rundunar Soji ta gargadi Jami’anta kan jita-jitan juyin mulki
Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi sojoji da su kaucewa sanya hannun su cikin harkokin siyasa, ko kuma su gamu da fushin hukuma.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun rundunar Janar Sani Usman Kukasheka ya ce shugaban sojin Janar Tukur Burutai ya samu bayanan da ke nuna masa cewar wasu ‘yan siyasa sun tuntubi wasu kananan sojojin ba tare da cikaken bayani a kai ba
Janar Kukasheka ya ce duk sojan da ke sha’awar sanya hannu cikin siyasa na iya aje aikin sa domin tsunduma cikin siyasar.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an sanar da babban hafsan sojin kasar da mukadashin shugaban kasa Yemi Osibanjo cewa ana shiryawa gwamnati manakisa, dalilan da ya sa suka alkawarta shawo kan lamarin.
An shafe shekaru 18 ana tafiyar da mulkin demokrudiya a Najeriya tun bayan karbe iko daga sojoji a shekarar 1999 cikin kwanciyar hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu