Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan matan Chibok sun ki amincewa a ceto su daga Boko Haram

Wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta yi garkuwa da su a Najeriya sun ki amincewa a ceto su daga hannun kungiyar duk da shafe fiye da shekaru uku a tsare.

Akwai 'yan matan Chibok 113 da Boko Haram ke ci gaba da tsare su
Akwai 'yan matan Chibok 113 da Boko Haram ke ci gaba da tsare su AFP
Talla

Daya daga cikin masu shiga tsakanin gwamnati da kungiyar don ganin an sako ‘yan matan na Chibok Zannah Mustapha ya bayyana cewa, wasu daga cikin matan sun ki shiga cikin jerin ‘yan mata 82 da gwamnatin Najeriya ta yi musayar su da mayakan Boko Haram a aranar Asabar da ta gabata.

Wannan dai ya haifar da dari-darin yiwuwar cusa wa ‘yan matan mummunar akidar Boko Haram, yayin da wasu bayanai ke cewa, akwai kuma yiwuwar tsoro ne ya hana su shiga jerin ‘yan matan 82.

Wasu kuwa na ganin cewa, watakila kunya ce ta hana su komawa cikin iyalansu don ci gaba da tsohuwar rayuwarsu.

A lokacin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, Mustapha wanda Lauye ne ya ce, bai samu damar zantawa da ‘yan matan ba don sanin dalilin da ya hana su amincewa da ceton.

A halin yanzu dai, akwai kimanin ‘yan matan makarantar Chibok 113 da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da tsare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.