Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Za'a fito da tsarin fallasa makaman da ke boye

Ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya fara nazari kan fito da tsarin fallasa makaman da aka boye ba bisa ka'ida ba a sassan kasar, da kuma tukwuicin da za’a bai wa wadda ya jagoranci samun nasarar hakan.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawarakan harkar tsaro Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawarakan harkar tsaro Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya. today.ng
Talla

Kakakin fadar gwamnatin Najeriya malam Garba Shehu ya sanar da haka a garin Abuja.

A cewarsa babban makasudin tsarin shi ne kawo karshen amfani da makamai a najeriya ba bisa ka’ida ba, da hakan ke jawo jefa wadanda basu ji ba basu gani ba cikin hadari.

Sabon yunkurin na zuwa ne watanni bayan kaddamar da tsarin fallasa kudaden da akai sama da fadi da su a Najeriya, wanda ke samun nasara, tun bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.