Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Za'a dauki sabbin jami'an 'yan sanda 155,000

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta gabatarwa shugaban kasar Muhammadu Buhari bukatar ya amince da shirinta na daukar sabbin jami’ai 155,000 cikin shekaru 5 masu zuwa.

Jami'an 'yan sandan Najeriya
Jami'an 'yan sandan Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mataimakin Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya, dake kula da sashin horarwa da bunkasa cigaban aikin mai shugabantar yankin kudu maso kudun Najeriya, Emmanuel Inyang, ya bayyana cigaban yayin da yake gabatar da jawabi a hedikwatar yan sandan jihar Bayelsa.

Inyang ya ce shirin daukar sabbin ‘yan sandan 31,000 a duk shekara har sau biyar, bangare ne na shirin rundunar ta kasa don ganin ta kai matakin cigaba da majalisar dinkin duniya ta kayyade.

Karkashin tsarin dokar aikin dan sanda da majalisar dinkin duniya ta fayyace, kamata yayi ace duk dan sanda 1 yana lura da mutane 400.

Sai dai yayinda yake Karin haske kan cigaban aikin a Najeriya mataimakin sifeton janar na ‘yan sandan kasar, ya ce duk dan sanda 1 a Najeriya, yana mataki ne na kula mutane 600.

Zalika wata majiya daga rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, rundunar na nazari kan fito da tsarin fallasa bayanan sirri don magance yaduwar makamai a boye zuwa sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.