Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Ana bukatar yi wa mutane miliyan 21 rigakafin cutar Sankarau a jihohi 5

Ministan Lafiya na Najeriya Farfesa Isaac Adewole ya bukaci gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ya hukunta duk wadanda aka kama da laifin saida maganin rigakafin cutar Sankarau da gwamnatin kasar ta samar kyauta.

Meningites outbreak in Nigeria has killed over 400
Meningites outbreak in Nigeria has killed over 400 africa-online.com
Talla

Farfesa Adewole ya bukaci daukar matakin ne yayin taron da ya halarta na sarakunan gargajiya da gwamnoni domin shawo kan cutar ta Sankarau, wanda ya gudana a garin Kaduna.

Ministan lafiyar yace ana bukatar dalar Amurka biliyan 1 domin yiwa akalla mutane miliyan 21 rigakafi a jihohi biyar, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Niger da kuma Katsina, da suke fuskantar annobar.

Farfesa Adewole ya kuma ce zuwa yanzu mutane 489 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar ta Sankarau a jihohin biyar, yayinda alkalumma suka nuna cewa mutane 4, 637 ne suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.