Isa ga babban shafi
Najeriya

Abubuwan da shirin farfado da tattalin arzikin Buhari ya Kunsa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin farfado da raya tattalin arzikin kasar wadda ya fuskanci koma baya da hawa-hawan firashi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Buhari da ke bayyana fatansa kan tasiri shirin a kasar, ya ce gwamnatinsa na da kudurin mayar da farfado da masana'antu da za ta kasance mai dogaro da kanta.

Shirin da masana tattalin arziki a Najeriya, ke cewa idan aka aiwatar da shi to babu shaka zai inganta rayuwar 'yan kasar.

Abubuwan da shirin ya kunsa.

Akwai Samar da ayyukan yi da gani ta yadda kasar zata shiga sahun kasashen da ke gwagwarmaya a duniya a fanin tattalin arziki.

Inganta Ma’aunin tattalin arzikin kasa da ke maki 2.19 a 2017 zuwa maki 7 a shekarar 2020.

Dai-daituwar hawa-hawan firashi da Kara samar da kudadden shigan gwamnati daga Naira Triliyan 2.7 zuwa Triliyan 4.7 kafin shekara ta 2020.

Tabbatuwar kananan sana’o’i samar da kudadden shiga, bunkasa yanayi samar da kudadden, Muhallin mai inganci da shugabanci da wadatuwar tsaro.

Akwai tsarin taimakawa kananan Bankuna da Masana'antu da Ma’aikatu da dai sauransu.

Gwamnati na son a dai na siyo tattacen man fetur daga ketare ta hanyar farfado da matatun man cikin gida, wanda zai kara kudadden shiga daga Naira Biliyan 700 a 2016 zuwa Triliyan 1.3 kowacce shekarar a 2017 zuwa Triliyan 1.45 a 2020.

Yawan gan-gan man da ake hakowa zai karu daga ganga miliyan 1.4 a 2016 zuwa miliyan 2.2 a 2017 da miliyan 2.5 kafin shekarar 2020.

Kana za a sake inganta batun Noma da wutan lantarki da Ma‘adanai da Sufuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.