Buhari zai kai ziyarce a ranar Litinin don kaddamar da gasar nuna kwarewar sarrafa kananan makamai tsakanin sojojin kasar ta wannan shekarar.
Ministan tsaro na kasar, Alhaji Mansur Dan Ali da kuma manyan hafsoshin soji na cikin wadanda za su yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa dajin na Sambisa.
A cikin watan Disamban bara ne dai, dakarun Najeriya suka yi nasarar fatattakar ‘yan Boko Haram daga Dajin.
A bangare guda, sojojin za su yi amfani da wannn gasar wajen gudanar da wasu ayyuka da suka hada da isar da magunguna ga 'yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin Bama da Konduga da Magumeri da ke jihar ta Borno.
Kazalika dakarun za su raba kayayyakin jin-kai ga 'yan gudun hijirar kafin daga bisani su gana da sarakunan gargajiya don tattaunawa kan sha'anin tsaro.