Isa ga babban shafi
Najeriya

Uwa ta sake tozali da danta bayan Boko Haram ta raba su

Kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta mika wani yaro mai shekaru 7 ga iyayensa a jihar Borno da ke Najeriya, bayan ta gano shi a sansanin ‘yan gudun hijirar Jamhuriyar Nijar.

Musa tare da iyayensa da kuma 'yan uwansa a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Borno a Najeriya
Musa tare da iyayensa da kuma 'yan uwansa a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Borno a Najeriya RFI hausa
Talla

Rikicin Boko Haram dai ya raba mutane da dama da iyalansu da suka hada da kananan yara da mata musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta gano Musa mai shekaru bakwai da haihuwa, in da ta mika shi ga iyayensa.

Mahaifiyar yaran ta bayyana farin cikinta da sake yin ido hudu da danta bayan ta debe tsammanin ganin shi.

A cikin wannan rahoton da Abdurrahman Gambo Ahmad ya hada mana, mahaifin yaran ya yi wa RFI hausa karin  bayani kann yadda Boko Haram ta yi musu lugudan wuta har ta tarwatsa danginsa. Kazalika za ku ji abin da ya yaran ke cewa dangane da zamansa a  sansanin Jamhuriyar Nijar.

01:27

Uwa ta sake tozali da danta bayan Boko Haram ta raba su

Dubban mutane ne dai rikicin Boko Haram ya tilasta wa kaurace wa gidajensu, in da wasu ke zaman gudun hijira a sansanoni daban daban a jihar Bornon Najeriya, yayin da wasu suka fice daga kasar zuwa kasashe masu makwabtaka da jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.