Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun soke mika sakamakon zabe da hannu - INEC

Hukumar zabe a Najeriya, INEC, ta sanar da bijiro da sabbin matakan Zabe da ta ke shirin kadamarwa a kokarin da ta ke wajen gani ta inganta yanayin zabe da gudanar da shi cikin sahihanci a shekarar 2019.

Akwatin kada kuri'a na hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa.
Akwatin kada kuri'a na hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa. nigeriannewsdirect.com
Talla

A zantawarsa da RFI Hausa, mai Magana da yawun hukumar ta INEC, Nick Dazan, ya ce daga cikin sabbin tsare tsaren akwai batun sauya yanayin rajistar zabe da raba katunan dindindin, sabanin wanda aka saba gani a shekarun baya.

Zalika Dazan ya ce INEC, ta soke mika sakamakon zabe hannu da hannu daga cibiyar kada kuri’u, a kokarinta na inganta tsarin gudanarwar zaben a shekarar 2019.

A cewar kakakin daga yanzu, hukumar zata koma ne kan tsarin karbar sakamako ta na’ura mai kwakwalwa, sabanin yawo da katunan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.