Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai kafa kwamiti don nazarin karin albashi a Najeriya

Ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba shugaban kasar Muhammadu Buhari zai kafa wani kwamiti mai mutane 29 domin shiga tattaunawa da kungiyoyin kwadagon kasar kan batun karin albashi ga ma’aikatan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari SEYLLOU / AFP
Talla

Manyan kungiyoyin kwadagon kasar TUC, NLC sun bukaci gwamnati da ta sake bitar albashin ma’aikatan kasar, domin samar da mafi kankantar albashi da zai kama daga Naira dubu 56.

Chris Ngige ya ce gwamnati na fadi tashin gani ta inganta koken da ma'aikatan ke yi kan albashi a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.