Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta rufe filin jirage na Abuja

Gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe tashar jiragen saman Abuja domin fara yin gyara kamar yadda tayi alkawari, yayin da sufurin jiragen sama zai koma filin sauka da tashin jirage da ke jihar Kaduna, wadda itace mafi kusa da Abuja.

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja Najeriya.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja Najeriya. guardian.ng
Talla

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika yace aikin zai kwashe watanni 6 anayi, amma an rufe filin jiragen sama na Abuja ne na tsawon makwanni shida kawai.

Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI Sirika ya yi Karin bayanin cewa aikin gyara titin da jirage ke sauka a filin Abujan shi ne zai dauki makwanni shida, yayinda sauran ayyukan sassan filin jirgin na Abuja zai kwashe watanni 6.

A cewar Ministan sufurin ya ce daukar wannan mataki ko salo na gudanar da aikin titin saukar jiragen, da sauran sassan filin, ya bada damar kaucewa bin hanyar gyaran filin jiragen na Abuja da zata shafe akalla shekaru biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.