Isa ga babban shafi
Najeriya

An dakile shirin kai harin bam a Gombe

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kama wasu ‘yan kasar Chadi uku da suke zargi da shirya kai harin bama-bamai a garin Gombe.

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar dakile shirin kai harin bam a jahar Gombe
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar dakile shirin kai harin bam a jahar Gombe ( Photo : Reuters )
Talla

Daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce sun yi nasarar kama mutanen uku ne tare da rundunar ‘yan Sandan farin kaya ta DSS, kuma sun fito ne daga bangaren Albarnawi, daya daga cikin jagororin kungiyar Boko Haram.

Daraktan ya bayyana sunayen mutanen da suka hada da Bilal Muhammed Umar da Bashir Muhammed da kuma Muhammad Maigari Abubakar.

Jahar Gombe da ke yakin arewacin Najeriya na daga cikin jihohin da suka yi fama da hare-haren mayakan Kungiyar Boko Haram.

Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin dakile kungiyar da yanzu haka ta yi sanadiyar rayukan mutane fiye da dubu biyu baya ga asarar tarin dukiya da kuma mutane fiye da miliyan daya da suka rasa matsuguninsu a wannan yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.