Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta kwace motoci daga tsohon shugaban hukumar kwastam

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, ta sanar da kwace wasu motocin kasaita 17, daga hannun tsohon shugaban hukumar kwastam Abdullahi Inde Dikko.

Tsohon Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya
Tsohon Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya nigeriantell
Talla

Mai Magana da yawun hukumar Wilson Uwujeran yace an gano motocin ne a wani gida da Dikko ya mallaka dake Kaduna, bayan bayannan da suka samu da ke cewa an boye kudi da dukiyar sata a ciki.

Uwujeran yace tuni aka kwashe motocin zuwa ofisoshin hukumar dake Kaduna da Kano.

Jami’in ya kara da cewa mutane biyu da suka kama a yayin da suka kai sumamen, suna taimaka musu wajen gudanar da bincike mai zurfi, kan zargin da ake wa tsohon shugaban hukumar ta Kwastam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.