Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya zata binciki kashe wasu 'yan kasar a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta bawa ofishin jakadancinta da ke kasar Afrika ta Kudu umarnin gudanar da bincike kan kashe wasu ‘yan Najeriya da aka yi, sakamakon nuna musu kyama.

Wasu 'yan Afrika ta Kudu da ke nunawa baki kyama
Wasu 'yan Afrika ta Kudu da ke nunawa baki kyama ibtimes.co.uk
Talla

Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Abassada Sola Enikanolaiye ya ce kafin satin da ake ciki ya kare ya ke sa ran samun rahoton binciken.

A ranar Alhamis da Juma’a ne dai wasu ‘yan kasar Afrika ta Kudun a birnin Pretoria suka afkawa wa wasu ‘yan Najeriya, inda suka kashe wasu tare da sace musu dukiya mai yawa.

Akalla ‘yan Najeriya 100 ne aka kashe daga shekaru biyu baya kawo yanzu a Afrika ta Kudu, sakamakon nunawa baki kyama da wasu ‘yan kasar ke yi.

A shekara ta 2015 wasu 'yan Afrika ta Kudu sun afkawa baki da aiki ko kasuwanci a kasar da hare hare inda suka kashe wasu bayan barnata dukiya mai tarin yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.