Isa ga babban shafi
Najeriya

Osinbajo ya sanya hannu kan sabbin dokoki a Najeriya

Mukadashin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbanjo, ya sanya hannu kan sabon dokar Fansho da Majalisa ta yi wa gyara da kuma wasu sabbin dokoki 6 da ya tsallake karatun ta. 

Mukadashin Shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo na aiwatar da ayyuka dama a kasar.
Mukadashin Shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo na aiwatar da ayyuka dama a kasar.
Talla

Mataimakin shugaban kasa na musamman a kan harkokin majalissu, Sanata Ita Enang ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Mista Osinbanjo da ke tafiyar da mulkin kasar a madadin shugaba Buhari, da ya tsawaita hutunsa a birnin London, ya aiwatar da ayyuka da dama a bayan shugaban.

Sauran dokokin 6 da ya sanyawa hannu a cewar Sanata Enang, sun hada da tsaro da tantace fina-finai da kotunan.

Raguwan kuma sune Hukumar nazarin kimiyar kasa da za a samar da kuma gyara a hukumar jingina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.