Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a mayarwa Gwamnatin Najeriya da Naira billiyan 35

Kotu a Najeriya ta bada umurnin mallakawa Gwamnatin kasar kudaden da suka kai naira biliyan 35 da aka gano mallakar tsohuwar Ministan albarkatun man kasar Diezani Allison-Madueke .

Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun man Najeriya
Diezani Allison-Madueke, Tsohuwar ministan albarkatun man Najeriya AFP / Wole Emmanuel
Talla

Mai shari’a Musulim Hassan dake birnin Lagos dake kudancin kasar, ya bada umurnin kamar yadda hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin zagon kasa EFCC ta bukata saboda gano cewar an mallake su ne ta hanyar da bata kamata ba.

A arewacin kasar a jihar Kano wata kotu dake yankin ta bada irin wannan umurnin kan kudin da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin man kasar Andrew Yakubu da suka kai sama da Dala miliyan 9.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.