Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta maida martani kan shirin gangamin 2Face

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Legas Fatai Owoseni ya ce, ba zasu bada damar yin zanga zangar da aka shirya gudanarwa a jihar ba, kan halin matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Mawaki 2face Idibia
Mawaki 2face Idibia
Talla

A ranar Talatar da ta gabata, daya daga cikin shahararrun mawaka a Najeriya, 2Face Idibia, ta shafinsa na Twitter, ya bukaci masoyansa su fito don yin zanga zangar, a ranar 5 ga watan da muke ciki.

Sai dai Kwamshinan ‘yan sandan jihar Legas, Fatai Owseni, ya ce babu wata bukata ko neman izinin gudanar da wannan zanga zanga da wadanda ki shirin gudanar da ita suka gabatar.

Zalika Owseni ya ce suna da rahotanni na sirri da ke nuna cewa, wasu bata gari, suna yunkurin yin amfani da damar gudanar da zanga zangar, wajen tada zaune tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.