Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najariya sun kashe mutane 52 akan kuskure

Akalla mutane 52 da suka hada da fararen hula da ma'aikatan agaji sun rasa rayukansu sakamakon wani harin sama da sojojin Najeriya suka kai cikin kuskure kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno.  

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai hari cikin kuskure kan wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar
Rundunar sojin saman Najeriya ta kai hari cikin kuskure kan wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar
Talla

Lamarin ya auku ne a kauyen Rann da ke karamar hukumar Kala-Balge a daidai lokacin da ake raba wa 'yan gudun hijirar abinci, abin da kuma ya yi sanadiyar jikkatar mutane 120 kamar yadda kungiyar likitoci ta MSF ta tabbatar.

Babban kwamanda na Operation Lafia Dole, Manjo Janar Lucky Irabor ya kira taron manema labarai cikinsu har da RFI hausa, in da ya shaida cewa, an kai harin ne bayan labarin da suka samu da ke cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram na haduwa a karamar hukumar ta  Kala-Balge.

Janar Irabor ya kara da cewa, wannan ne ya tilasta musu daukan matakin aike wa da sojin sama don murkushe mayakan na Boko Haram da aka tarwatsa su daga dajin sambisa da ya kasance babbar matattararsu a can baya.

Harin wanda aka kai a wannan Talata, ya shafi ma’aikatan kungiyar likitoci mai zaman kanta ta MSF da kuma kungiyar bayar da agaji ta duniya Red Cross.

Kawo yanzu rundunar sojin kasar ba ta fitar da nata alkaluman ba dangane da adadin wadanda suka mutu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya damu matuka da samun wannan mummunan labarin, yayin da ya aike da sakon ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.