Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta lalata asibitocin Borno

Hukumar lafiyar ta duniya WHO ta ce, a cikin shekaru 7 an lalata kashi daya cikin uku na asibitocin da ake da su a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sakamakon ayyukan Boko Haram. 

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da Boko Haram ta kai a wata kasuwa.
Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da Boko Haram ta kai a wata kasuwa. REUTERS/Stringer
Talla

Rahoton ya bayyana cewa, a wannan yanki akwai asibitoci manya da kanana har guda 743, to amma a cikin wadannan shekaru an rusa kashi daya cikin uku na wadannan cibiyoyi na kiwon lafiya.

WHO ta ce, ta samu wadannan alkaluma ne sakamakon wani binciken hadin-giwa da ta gudanar tare da ma’aikatar lafiya ta jihar Borno, kuma kashi 35 cikin 100 na asibitocin an lalata su baki daya, sai kashi 29 da ba sa tafiyar da aiki yadda ya kamata, yayin da sauran kashi 34  ne kawai ke iya kula da jama’a.

Mista Wondi Alemu, shugaban ofishin hukumar lafiya ta duniya a Najeriya ya ce, rashin tsaro a yankin ya sa jami’an kiwon lafiya guje wa wureren ayyukansu, yayin da sauran asibitocin ke fama da rashin kayan aiki, magunguna da kuma ruwan sha.

A wani rahoto da ta fitar a kwanakin baya, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yara dubu 75 za su iya rasa rayukansu a yankin a cikin shekara mai zuwa matukar dai ba a samar da agaji ga jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.