Isa ga babban shafi
Najeriya-Tattalin Arziki

Najeriya: Kudurin dokar ware Naira Triliyan 1.4 don raya mazabu ya wuce karatu na biyu

Wani kudurin doka da ke neman ware kashi 20 daga cikin kasafin kudin tarayyar Najeriya domin ayyukan raya mazabu, ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattawan kasar. 

Zauren Majalisar Dattawan Najeriya
Zauren Majalisar Dattawan Najeriya
Talla

‘Yar majalisar dattawa da ke wakiltar jihar Anambra Stella Oduah ce ta gabatar da kudurin, da ke neman ware kashi 20 na kasafin kudin Najeriya domin ayyukan raya mazabu a sassan kasar.

Idan aka amince da kudurin a matsayin doka, ayyukan raya mazabu da ‘yan majalisun ke kula da su, zasu lakume akalla Naira triliyan 1 da biliyan 400 daga cikin kasafin kudin naira Triliyan 7 da biliyan 300 da gwamnatin Najeriya zata gabatar na 2017.

Bisa al’ada a Najeriya ‘yan majalisu na amfani da damar kudaden da aka ware don ayyuka a mazabu wajen, jagorantar gina hanyoyi, gyara makarantu, samar da rijiyoyin birtsatsai, sai kuma tallafawa jama’a da kayayyakin sana’a kamar kekunan dinki, injunan markade dana saka.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, ya mika kudurin zuwa kwamitin da ke aiki kan kasafin kudin kasa domin nazari a kai, ya kuma gabatar da rahotonsa cikin makwanni 4.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.