Gwamnatin Najeriya zata gabatar da kasafin kudi na Naira triliyan 7
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, ya ce nan da kwanaki goma ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekara ta 2017.
Wallafawa ranar:
Saraki ya ce a wannan karon ba za’a samu makamancin tsaikon da aka fuskanta ba daga Majalisar, wajen amincewa da kasafin, na Naira tiriliyan 7.
A ranar Alhamis din data gabata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da Sanata Bukola Saraki kan shirye shiryen gabatar da safin kudin na sabuwar shekara ga majalisar kasar.
Tun a ranar Larabar da ta gabata kuma, Majalisar zartaswar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin da za’a gabatarwa Majalisar kasar.
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jaddada cewa dole a samu hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnatin kasar, da kuma masu ruwa da tsaki a fannonin da ke zaman kansu, domin sabon kasafin kudin yayi tasiri wajen samar da cigaba a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu